| 19.11.2008 | 09:00 UTC
Amnesty ta zargi Rasha da Georgia da laifin kasa kare fararen hula
Ƙungiyar agaji ta Amnesty International ta zargi ƙasashen Rasha da Georgia da manyan laifuka na take hakkin bil Adama a lokacin yaƙinsu na kwanaki biyar a watan Agusta.Ƙungiyar ta ce dukkaninsu ɓangarorin biyu sun gagara kare fararen hula da yaƙin ya rutsa da su.Amnesty ta ce har yanzu akwai 'yan asalin Georgia fiye da 20,000 da suka gagara komawa gida haka kuma da dama daga ɓangarorin biyu sun taradda an wawashe gidajensu.Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ƙasashen biyu da su nemi hukumar tantance gaskiya ta ƙasa da ƙasa da ta ƙaddamar da bincike kan abin da ya faru.A halin da ake ciki kuma jakadan Georgia a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira da gudanar da bincike don tabbatar da wace ƙasa ce tsakanin Rasha da Georgia da ta fara takanar faɗa a Ossetia ta Kudu,wanda ya lalata danganta tsakanin Rasha da ƙasashen yammacin duniya.







